Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 66

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura.

Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

Ku rera ɗaukaka ga sunansa;

ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!

Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke!

Ikonka da girma yake

har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

Dukan duniya sun rusuna a gabanka

suna rera yabo gare ka,

suna rera yabo ga sunanka.” Sela

Ku zo ku ga abin da Allah ya yi,

ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum!

Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa,

sun wuce cikin ruwaye da ƙafa,

ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.

Yana mulki har abada ta wurin ikonsa,

idanunsa suna duban al’ummai,

kada ’yan tawaye su tayar masa. Sela

Ku yabi Allahnku, ya mutane,

bari a ji ƙarar yabonsa;

ya adana rayukanmu

ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi.

Gama kai, ya Allah, ka gwada mu;

ka tace mu kamar azurfa.

Ka kawo mu cikin kurkuku

ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.

Ka bar mutane suka hau a kawunanmu;

mun bi ta wuta da ruwa,

amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.

Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa

zan kuwa cika alkawurana gare ka,

alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa

sa’ad da nake cikin wahala.

Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka

da kuma baye-baye na raguna;

zan miƙa bijimai da awaki. Sela

Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah;

bari in faɗa muku abin da ya yi mini.

Na yi kuka gare shi da bakina;

yabonsa yana a harshena.

Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata,

da Ubangiji ba zai saurara ba;

amma tabbatacce Allah ya saurara

ya kuma ji muryata a cikin addu’a.

Yabo ga Allah,

wanda bai ƙi addu’ata ba

ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.