Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 65

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa.

Yabo ya dace1 da kai, ya Allah, a Sihiyona;

a gare ka za mu cika alkawuranmu

Ya kai wanda yake jin addu’a

a gare ka dukan mutane za su zo.

Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu,

ka gafarta2 laifofinmu.

Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa

ka kawo kusa don su zauna a filayenka!

Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka,

na haikalinka mai tsarki.

Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci,

Ya Allah Mai Cetonmu,

begen dukan iyakar duniya

da kuma na tekuna masu nesa,

wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka,

bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,

wanda ya kwantar da rurin tekuna,

rurin raƙumansu,

da kuma tumbatsar al’ummai.

Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka;

inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe

kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.

Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa;

kana azurta ta a yalwace.

Rafuffukan Allah sun cika da ruwa

don su ba mutane hatsi,

don haka ne ka ƙaddara.3

Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta;

ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.

Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka,

amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.

Makiyayan hamada sun cika har suna zuba;

tuddai sun rufu da murna.

Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna

kwari kuma sun cika da hatsi;

suna sowa don farin ciki.

Source notes (3)
  1. Footnote Ko kuwa kan jira; ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba.
  2. Footnote Ko kuwa ka yi kafara domin
  3. Footnote Ko kuwa don haka ne ka shirya ƙasar

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.