Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 125

Waƙar haurawa.

Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,

wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.

Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,

haka Ubangiji ya kewaye mutanensa

yanzu da har abada kuma.

Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance

a kan ƙasar da take rabon adalai ba,

domin kada masu adalci su yi amfani

da hannuwansu su aikata mugunta.

Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,

ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.

Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi

Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta.

Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.