Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020
Zabura 124
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba,
bari Isra’ila yă ce,
da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba
sa’ad da aka auka mana,
sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu,
ai, da sun haɗiye mu da rai;
da rigyawa ta kwashe mu,
da ambaliya ta rufe mu.
Da ruwa mai hauka
ya share mu ƙaf.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.
Mun tsira kamar tsuntsu
daga tarkon mai farauta;
an tsinke tarko,
muka kuwa tsira.
Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,
Wanda ya yi sama da ƙasa.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.
Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.