Skip to content
BibleKenya

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Zabura 51

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba.

Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;

bisa ga tausayinka mai girma

ka shafe laifofina.

Ka wanke dukan kurakuraina

ka tsarkake ni daga zunubina.

Gama ina sane da laifofina

zunubaina kuma kullum suna a gabana.

Kai kaɗai na yi wa zunubi

na yi abin da yake mugu a idonka,

ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana

aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa

mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;

ka koya mini hikima a wuri can ciki.

Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab;

ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.

Bari in ji farin ciki da murna;

bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina

ka kuma shafe dukan kurakuraina.

Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,

ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.

Kada ka fid da ni daga gabanka

ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.

Ka mayar mini farin cikin cetonka

ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.

Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka,

masu zunubi kuma za su komo gare ka.

Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah,

Allahn da ya cece ni,

harshena kuwa zai rera adalcinka.

Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana,

bakina kuwa zai furta yabonka.

Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo;

ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu;

karyayyiya da kuma zuciya mai tuba,

Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara;

ka gina katangar Urushalima.

Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci,

hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka;

sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Source: eBible.org. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-10-25.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.