Skip to content
BibleKenya

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Zabura 48

Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza.

Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo,

a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.

Kyakkyawa ce cikin tsayinta,

abin farin cikin dukan duniya.

Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon1 ne Dutsen Sihiyona,

birnin2 Babban Sarki.

Allah yana cikin fadodinta;

ya nuna kansa mafaka ce gare ta.

Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni,

sa’ad da suka yi gaba tare,

sun gan ta suka kuwa yi mamaki;

suka gudu don tsoro.

Rawar jiki ya kama su a can,

zafi kamar na mace mai naƙuda.

Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish

da iskar gabas ta wargaje.

Yadda muka ji,

haka muka gani

a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki,

a cikin birnin Allahnmu.

Allah ya sa ta zauna lafiya

har abada. Sela

Cikin haikalinka, ya Allah,

mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.

Kamar sunanka, ya Allah,

yabonka ya kai iyakokin duniya;

hannunka na dama ya cika da adalci.

Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki,

ƙauyukan Yahuda suna murna

saboda hukuntanka.

Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta,

ku ƙirga hasumiyoyinta,

ku lura da katangarta da kyau,

ku dubi fadodinta,

don ku faɗe su

ga tsara mai zuwa.

Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin;

zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.

Source notes (2)
  1. Footnote Zafon yana nufin dutse mai tsarki ko kuwa gefen arewa.
  2. Footnote Ko kuwa duniya, Dutsen Sihiyona, a arewanci na

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Source: eBible.org. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-10-25.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.