Skip to content
BibleKenya

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Zabura 44

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’ya’yan Kora maza. Maskil ne.

Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah;

kakanninmu sun faɗa mana

abin da ka aikata a kwanakinsu,

tun dā can.

Da hannunka ka kori al’ummai

ka kuma dasa kakanninmu;

ka ragargaza mutanen

ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.

Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar,

ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba;

hannun damanka ne, ƙarfin hannunka,

da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.

Kai ne Sarkina da kuma Allahna,

wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.

Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya;

ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.

Ba na dogara ga bakana,

takobina ba ya kawo nasara;

amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu,

ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.

A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini,

kuma za mu yabi sunanka har abada. Sela

Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu;

ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.

Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba,

kuma abokan gābanmu suka washe mu.

Ka ba da mu a cinye kamar tumaki

ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.

Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba

babu wata riba daga sayar da su da ka yi.

Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu,

abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.

Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai;

mutanen suna kaɗa mana kai.

Dukan yini ina cikin wulaƙanci,

fuskata kuma ta rufu da kunya

saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina,

saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.

Dukan wannan ya faru da mu,

ko da yake ba mu manta da kai ba

ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.

Zukatanmu ba su juya baya;

ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.

Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji

ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.

Da a ce mun manta da sunan Allahnmu

ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,

da Allah bai gane ba,

da yake ya san asiran zuciya?

Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini;

aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.

Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci?

Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.

Me ya sa ka ɓoye fuskarka

ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?

An kai mu ƙasa zuwa ƙura;

jikunanmu sun manne da ƙasa.

Ka tashi ka taimake mu;

ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Source: eBible.org. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-10-25.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.