Skip to content
BibleKenya

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Farawa 10

Tsarin Al’ummai

Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.

Mutanen Yafet

’Ya’yan1 Yafet maza su ne,

Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.

’Ya’yan Gomer maza su ne,

Ashkenaz, Rifat, da Togarma.

’Ya’yan maza Yaban su ne,

Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)

Mutanen Ham

’Ya’yan Ham maza su ne,

Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.

’Ya’yan Kush maza su ne,

Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.

’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne,

Sheba da Dedan.

Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji. Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar. Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.

Mizrayim shi ne mahaifin

Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa, Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.

Kan’ana shi ne mahaifin,

Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa, Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa.

Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.

Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

Mutanen Shem

Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.

’Ya’yan Shem maza su ne,

Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.

’Ya’yan Aram maza su ne,

Uz, Hul, Geter da Mash.

Arfakshad ne mahaifin2 Shela.

Shela kuma shi ne mahaifin Eber.

Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.

Aka ba wa ɗaya suna Feleg,3 gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.

Yoktan shi ne mahaifin,

Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera, Hadoram, Uzal, Dikla, Obal, Abimayel, Sheba, Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.

Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.

Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.

Source notes (3)
  1. Footnote ’Ya’ya maza na iya nufin zuriyoyi Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 3, 4, 6, 7, 20-23, 29 da 31.
  2. Footnote Da Ibraniyanci; Seftuwajin, mahaifin shi ne Kainan, Kainan kuwa shi ne mahaifin
  3. Footnote Feleg yana nufin rarrabuwa.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Source: eBible.org. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-10-25.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.