Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zakariya 10

Ubangiji zai lura da Yahuda

Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara;

Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari.

Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama

yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.

Gumaka suna maganganun ruɗu,

masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya,

suna faɗa mafarkan ƙarya

suna ba da ta’aziyyar banza.

Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki

waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.

“Ina fushi da makiyayan,

zan kuma hukunta shugabannin;

gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura

da garkensa, wato, gidan Yahuda,

zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.

Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito,

daga gare shi za a samu abin kafa tenti,

daga gare shi za a sami bakan yaƙi,

daga gare shi za a sami kowane mai mulki.

Tare za su1 zama kamar mutane masu ƙarfi

suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi.

Domin Ubangiji yana tare da su,

za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.

“Zan ƙarfafa gidan Yahuda

in kuma ceci gidan Yusuf.

Zan maido da su

domin ina jin tausayinsu.

Za su zama kamar

ban taɓa ƙinsu ba,

gama ni ne Ubangiji Allahnsu

zan kuma amsa musu.

Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi,

zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi.

’Ya’yansu za su gani su yi murna;

zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.

Zan ba da alama

in kuma tattara su.

Ba shakka zan fanshe su;

za su yi yawa kamar yadda suke a dā.

Ko da yake na warwatsa su cikin mutane,

duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni.

Su da ’ya’yansu za su rayu,

za su kuwa komo.

Zan komo da su daga Masar

in kuma tattara su daga Assuriya.

Zan kawo su Gileyad da Lebanon,

har wuri yă kāsa musu.

Za su ratsa cikin tekun wahala;

zan kwantar da raƙuman teku

dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe.

Za a ƙasƙantar da Assuriya,

sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.

Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji

kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,”

in ji Ubangiji.

Source notes (1)
  1. Footnote Ko kuwa mai mulki, dukansu tare. 5 Su

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.