Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020
Zabura 96
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;
ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;
ku yi shelar cetonsa kowace rana.
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;
tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,
amma Ubangiji ne ya yi sammai.
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;
ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.
Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai
ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.
Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;
ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.
Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;
ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.
Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.”
Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba;
zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.
Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;
bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.
Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;
za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,
yana zuwa don yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya cikin adalci
mutane kuma cikin amincinsa.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.
Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.