Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020
Zabura 93
Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka;
Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi.
An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.
An kafa kursiyin tun da daɗewa;
kana nan tun fil azal.
Tekuna sun taso, ya Ubangiji,
tekuna sun ta da muryarsu;
tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.
Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye,
mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku,
Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.
Ƙa’idodinka suna nan daram;
tsarki ya yi wa gidanka ado
har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.
Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.