Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 90

LITTAFI NA HUƊU

Zabura 90–106

Addu’ar Musa Mutumin Allah.

Ubangiji kai ne mazauninmu

cikin dukan zamanai.

Kafin a haifi duwatsu

ko a fid da ƙasa da duniya,

daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.

Ka komar da mutane zuwa ƙura,

kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.”

Gama shekaru dubu a gabanka

kamar kwana ɗaya ne da ya wuce,

ko sa’a guda na dare.

Ka share mutane cikin barcin mutuwa;

suna kama da sabuwa ciyawar safiya,

ko da yake da safe takan yi sabuwar huda

da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane.

An cinye mu ta wurin fushinka

mun kuma razana ta wurin hasalarka.

Ka ajiye laifinmu a gabanka,

asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.

Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka;

mun gama shekarunmu da nishi.

Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne,

ko tamanin, in muna da ƙarfi;

duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai,

gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.

Wa ya san ƙarfin fushinka?

Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai.

Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,

don mu sami zuciyar hikima.

Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba?

Ka ji tausayin bayinka.

Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa,

don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.

Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba,

kamar yawan shekarun da muka ga wahala.

Bari a nuna ayyukanka ga bayinka,

darajarka ga ’ya’yansu.

Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu;

ka albarkaci mana aikin hannuwanmu,

I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.