Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 81

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf.

Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu;

ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!

Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga,

ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.

Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata,

da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;

wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila,

farilla ta Allah na Yaƙub.

Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf

sa’ad da ya fito daga Masar.

Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.

Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku;

an ’yantar da hannuwansu daga kwando.

Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku,

na amsa muku daga girgijen tsawa;

na gwada ku a ruwan Meriba. Sela

“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku,

in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!

Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku;

ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.

Ni ne Ubangiji Allahnku

wanda ya fitar da ku daga Masar.

Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.

“Amma mutanena ba su saurare ni ba;

Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.

Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare

don su bi dabararsu.

“A ce mutanena za su saurare ni,

a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,

da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu

in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!

Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki,

hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.

Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau;

da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.