Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020
Zabura 60
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri.
Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu;
ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!
Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta;
ka daure karayarta, gama tana rawa.
Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala;
ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.
Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta
don a buɗe gāba da baka. Sela
Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama,
domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,
“Da nasara zan rarraba Shekem
in kuma auna Kwarin Sukkot.
Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne;
Efraim shi ne hular kwanona,
Yahuda kuma sandar mulkina.
Mowab shi ne kwanon wankina,
a kan Edom zan jefa takalmina;
a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”
Wa zai kawo ni birnin katanga?
Wa zai bishe ni zuwa Edom?
Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu
ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba,
gama taimakon mutum banza ne.
Tare da Allah za mu yi nasara,
zai kuma tattake abokan gābanmu.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.
Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.