Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 52

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.”

Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum?

Me ya sa kake fariya dukan yini,

kai da kake abin kunya a idanun Allah?

Harshenka kan shirya hallaka;

yana nan kamar reza mai ci,

kana ta ruɗu.

Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,

ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela

Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,

Ya kai harshe mai ruɗu!

Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.

Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;

zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela

Masu adalci za su ga su ji tsoro;

za su yi masa dariya, suna cewa,

“Yanzu, ga mutumin

da bai mai da Allah mafakarsa ba

amma ya dogara a yawan arzikinsa

ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”

Amma ni kamar itace zaitun ne

ina haɓaka a gidan Allah;

na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah

har abada abadin.

Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;

a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.

Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.