Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 36

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji.

Akwai magana a cikin zuciyata

game da zunubin mugu.

Babu tsoron Allah

a idanunsa.

Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne

wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.

Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu;

ya daina zama mai hikima da yin alheri.

Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta;

yakan sa kansa ga aikata zunubi

kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.

Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai,

amincinka har sararin sammai.

Adalcinka yana kama da manyan duwatsu,

hukuncinka kamar zurfi mai girma.

Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa!

Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

Suna biki a yalwar gidanka;

kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.

Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai

cikin haskenka mukan ga haske.

Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka,

adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.

Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini,

ko hannun mugu ya kore ni.

Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi,

a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.