Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 29

Zabura ta Dawuda.

Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,

ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;

ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye;

Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,

Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.

Muryar Ubangiji mai iko ce;

muryar Ubangiji da girma take.

Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon.

Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.

Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi,

Siriyon1 kuma kamar ɗan jakin jeji.

Muryar Ubangiji ta buga

da walƙatar walƙiya.

Muryar Ubangiji ta girgiza hamada

Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.

Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak2

ya kakkaɓe itatuwan kurmi.

Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”

Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa;

Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.

Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;

Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.

Source notes (2)
  1. Footnote Wato, Dutsen Hermon
  2. Footnote Ko kuwa Ubangiji ya sa barewa ta haihu.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.