Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 17

Addu’a ce ta Dawuda.

Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci;

ka saurari kukata.

Ka kasa kunne ga addu’ata,

ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.

Bari fiffitawata tă zo daga gare ka;

bari idanunka su ga abin da yake daidai.

Ko ka duba zuciyata,

ka kuma bincike ni da dare,

ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba;

na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.

Game da ayyukan mutane kuwa,

ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina

daga hanyoyin tashin hankali.

Sawuna sun kama hanyoyinka

ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.

Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini;

ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.

Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki,

kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu

da hannunka na dama.

Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido;

ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka

daga mugaye waɗanda suke kai mini hari,

daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.

Sun rufe zukatansu marar tausayi,

da bakunansu suna magana da fariya.

Sun sa mini ido, yanzu sun kewaye ni,

a shirye suke, su jefa ni a ƙasa.

Suna kama da zaki mai yunwan abinci,

kamar babban zaki mai fako a maɓuya.

Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su;

ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka.

Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan,

daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne.

Kakan cika yunwan waɗanda kake so;

’ya’yansu suna da isashe

suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu.

Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka;

sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.