Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 149

Yabi Ubangiji.1

Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,

yabonsa a cikin taron tsarkaka.

Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu;

bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.

Bari su yabi sunansa tare da rawa

suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.

Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa;

yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.

Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma

su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.

Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu

takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,

don su ɗau fansa a kan al’ummai

da kuma hukunci a kan mutane,

don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi,

manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,

don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu.

Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa.

Yabi Ubangiji.

Source notes (1)
  1. Footnote Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 9.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.