Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020
Zabura 131
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji,
idanuna ba sa fariya;
ban dami kaina da manyan al’amura ba
ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
Amma na haƙura na kuma kwantar da raina;
kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa,
kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji
yanzu da har abada kuma.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.
Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.