Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Zabura 114

Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar,

gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,

Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah,

Isra’ila mallakarsa.

Teku ya kalla ya kuma gudu,

Urdun ya juye da baya;

duwatsu suka yi tsalle kamar raguna,

tuddai kamar tumaki.

Me ya sa, ya teku, kika gudu,

Ya Urdun, ka juya baya,

ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna,

ku tuddai, kamar tumaki?

Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji,

a gaban Allah na Yaƙub,

wanda ya juye dutse ya zama tafki,

dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.