Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mika 5

An yi alkawarin mai mulki daga Betlehem

Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa,1

gama an kewaye mu da yaƙi.

Za su bugi kumatun mai mulkin

Isra’ila da sandar ƙarfe.

“Amma ke, Betlehem ta Efrata,

ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki2 a Yahuda,

daga cikinki wani zai zo domina

wanda zai yi mulkin Isra’ila,

wanda asalinsa3

tun fil azal ne.”4

Saboda haka za a yashe Isra’ila

har sai wadda take naƙuda ta haihu

sauran ’yan’uwansa kuma sun dawo

su haɗu da Isra’ilawa.

Zai tsaya yă yi kiwon garkensa

da ƙarfin Ubangiji,

cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa.

Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa

za tă kai har ƙarshen duniya.

Zai kuma zama salamarsu.

Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari

suka tattake kagarunmu,

za mu tā da makiyaya bakwai,

har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.

Za su yi mulkin5 ƙasar Assuriya da takobi,

ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi.6

Zai cece mu daga hannun Assuriyawa

sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari

suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.

Raguwar Yaƙub za tă kasance

a tsakiyar mutane masu yawa

kamar raɓa daga Ubangiji,

kamar yayyafi a kan ciyawa,

wanda ba ya jiran mutum

ko kuma yă dakata wa ɗan adam.

Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai,

a cikin mutane masu yawa,

kamar zaki a cikin sauran namun jeji,

kamar ɗan zaki cikin garken tumaki,

wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu,

ba kuwa wanda zai cece su.

Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka,

za a hallaka maƙiyanka duka.

“A wannan rana,” in ji Ubangiji

“Zan hallaka dawakanku daga cikinku,

in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.

Zan hallaka biranen ƙasarku

in yi rugu-rugu da dukan katangunku.

Zan kawar da maitarku,

ba za a ƙara yin sihiri ba.

Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa

da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku,

nan gaba ba za ku ƙara rusuna

wa aikin hannuwanku ba.

Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku7

in kuma rurrushe biranenku.

Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala

a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”

Source notes (7)
  1. Footnote Ko kuwa Ƙara ƙarfin katangarki, ya katangan birni
  2. Footnote Ko kuwa masu mulki
  3. Footnote Da Ibraniyanci fitowa daga
  4. Footnote Ko kuwa daga madawwamin kwanaki
  5. Footnote Ko kuwa ragargaza
  6. Footnote Ko kuwa Nimrod a bakin ƙofofinta
  7. Footnote Wato, alamar alliyar Ashera

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.