Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Ezra 2

Waɗanda suka dawo daga bauta

(Nehemiya 7.4-73)

Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu. Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana).

Ga jerin mazan mutanen Isra’ila.

Zuriyar

Farosh mutum 2,172

ta Shefatiya 372

ta Ara 775

ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812

ta Elam 1,254

ta Zattu 945

ta Zakkai 760

ta Bani 642

ta Bebai 623

ta Azgad 1,222

ta Adonikam 666

ta Bigwai 2,056

ta Adin 454

ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98

ta Bezai 323

ta Yora 112

ta Hashum 223

ta Gibbar 95.

Mutanen

Betlehem 123

na Netofa 56

na Anatot 128

na Azmawet 42

na Kiriyat Yeyarim,1 da Kefira Beyerot 743

na Rama da Geba 621

na Mikmash 122

na Betel da Ai 223

na Nebo 52

na Magbish 156

na ɗayan Elam ɗin 1,254

na Harim 320

na Lod, da Hadid da Ono 725

na Yeriko 345

na Sena’a 3,630.

Firistoci.

Zuriyar

Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973

ta Immer 1,052

ta Fashhur 1,247

ta Harim 1,017.

Lawiyawa.

Lawiyawa na zuriyar

Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74.

Mawaƙa.

Zuriyar

Asaf mutum 128.

Masu tsaron haikali.

Zuriyar

Shallum, Ater, Talmon,

Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139.

Ma’aikatan haikali.

Zuriyar

Ziha, Hasufa, Tabbawot,

Keros, Siyaha, Fadon,

Lebana, Hagaba, Akkub,

Hagab, Shamlai, Hanan,

Giddel, Gahar, Reyahiya,

Rezin, Nekoda, Gazzam,

Uzza, Faseya, Besai,

Asna, Meyunawa, Nefussiyawa,

Bakbuk, Hakufa, Harhur,

Bazlut, Mehida, Harsha,

Barkos, Sisera, Tema,

Neziya da Hatifa.

Zuriyar bayin Solomon.

Zuriyar

Sotai, Hassoferet, Feruda,

Ya’ala, Darkon, Giddel,

Shefatiya, Hattil,

Fokeret-Hazzebayim, da Ami.

Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392.

Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba.

’Yan zuriyar

Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652.

Daga cikin firistoci kuma,

zuriyar

Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna).

Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne. Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.

Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200. Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245, raƙuma 435, da jakuna 6,720.

Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake. Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100.

Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.

Source notes (1)
  1. Footnote Dubi Seftuwajin (dubi kuma Neh 7.29); da Ibraniyanci Kiriyat Arim

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.