Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Amos 9

Za a hallaka Isra’ila

Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce,

“Bugi kan ginshiƙan

don madogaran ƙofa su girgiza.

Saukar da su a kan dukan mutane;

waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi.

Ba mutum guda da zai tsere,

babu wani da zai tsira.

Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari,

daga can hannuna zai fitar da su.

Ko da sun hau can sama

daga can zan sauko da su.

Ko da sun ɓuya a bisa Karmel,

a can zan farauce su in cafko.

Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku,

a can zan umarci maciji yă sare su.

Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta,

a can zan umarci takobi yă kashe su.

“Zan sa musu ido

don mugunta ba don alheri ba.”

Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,

shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke,

kuma dukan mazauna cikinta suna makoki,

ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu,

sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar,

shi da ya gina kyakkyawar fadarsa1 a cikin sammai

ya kuma kafa harsashenta2 a duniya,

shi da yakan kira ruwan teku

yă kuma kwarara su a bisa duniya,

Ubangiji ne sunansa.

“Ku ba Isra’ilawa ba ne,

daidai gare ni kamar yadda Kushawa suke?”3

In ji Ubangiji.

“Ban fito da Isra’ila daga Masar ba,

Filistiyawa kuma daga Kaftor4

Arameyawa kuma daga Kir ba?

“Tabbatacce idanun Ubangiji Mai Iko Duka

suna a kan mulkin nan mai zunubi.

Zan hallaka shi

daga fuskar duniya,

duk da haka ba zan hallaka

gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,”

in ji Ubangiji.

“Gama zan ba da umarni,

zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila

a cikin dukan ƙasashe

kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi

kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba.

Dukan masu zunubi a cikin mutanena

za su mutu ta wurin takobi,

wato, su masu cewa,

‘Masifa ba za tă fāɗo ko ta same mu ba.’

Maidowar Isra’ila

“A wannan rana zan maido

da tentin Dawuda da ya fāɗi.

Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage,

in kuma maido da kufansa

in gina shi kamar yadda yake a dā,

domin su mallaki raguwar Edom

da duk al’ummai da suke amsa sunana,”5

in ji Ubangiji shi wanda zai yi waɗannan abubuwa.

“Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji,

“sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi

mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi.

Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu

yă kuma kwararo daga tuddai.

Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta6 mutanena Isra’ila.

“Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu.

Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu;

za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu.

Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu,

ba kuwa za a ƙara tumɓuke su

daga ƙasar da na ba su ba,”

in ji Ubangiji Allahnku.

Source notes (6)
  1. Footnote Ma’anar Ibraniyanci don wannan zance babu tabbas.
  2. Footnote Ma’anar Ibraniyanci don wannan kalma babu tabbas.
  3. Footnote Wato, mutane daga yankin bisa na Nilu
  4. Footnote Wato, Kirit
  5. Footnote Da Ibraniyanci; Seftuwajin don raguwar mutane / da kuma dukan al’umman da ake kira da sunana za su nemi Ubangiji
  6. Footnote Ko kuwa zan maido da nasarar

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.