Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Sama’ila 8

Nasarorin Dawuda

(1 Tarihi 18.1-13)

Ana nan, sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar, ya kuma ƙwace ƙasar Meteg Amma daga hannun Filistiyawa.

Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji.

Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba. Wannan ya faru a lokacin da Hadadezer yake kan hanyarsa zuwa Kogin Yuferites don yă sāke mai da wurin a ƙarƙashin ikonsa. Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai1, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari.

Sa’ad da Arameyawan Damaskus suka zo don su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe dubu ashirin da biyunsu. Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi.

Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariya na shugabannin sojojin Hadadezer ya kawo Urushalima. Daga Teba2 da Berotai, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Sarki Dawuda ya kwashe tagulla masu yawan gaske.

Da Towu3 sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer, sai ya aiki ɗansa Yoram4 wurin Sarki Dawuda yă gaishe, yă kuma yi masa barka saboda nasarar da ya yi a kan Hadadezer, gama Hadadezer nan ya hana Towu sakewa. Yoram ya tafi ɗauke da kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan kayayyaki wa Ubangiji, yadda ya yi da zinariya, da kuma azurfa daga dukan al’umman da ya mallaka, wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba.

Dawuda kuwa ya ƙara zama shahararre bayan ya dawo daga kai wa ƙasar Aram hari, daga nan sai ya je ya karkashe mutanen Edom5 dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.

Ya ajiye rundunar sojoji ko’ina a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba wa Dawuda nasara a duk inda ya tafi.

Hafsoshin Dawuda

(1 Tarihi 18.14-17)

Dawuda ya yi mulkin dukan ƙasar Isra’ila, yana yin wa dukan jama’arsa shari’ar gaskiya da adalci. Yowab ɗan Zeruhiya ya zama shugaban sojoji; Yehoshafat ɗan Ahilud kuwa shi ne marubucin tarihi; Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare; Benahiya ɗan Yehohiyada ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, wato, sojoji masu gadin Dawuda, sa’an nan ’ya’yan Dawuda maza su ne mashawartan sarki.6

Source notes (6)
  1. Footnote Seftuwajin (duba kuma Naɗaɗɗun Littattafan Matacce Teku da kuma 1Tar 18.4); Nassin Masoretik kame mahayan keken yaƙinsa ɗari goma sha bakwai
  2. Footnote Dubi waɗansu rubuce-rubucen hannun Seftuwajin (dubi kuma 1Tar 18.8); Ibraniyanci Beta.
  3. Footnote Da Ibraniyanci Toi, wani suna na Towu; haka ma a aya 10.
  4. Footnote Wani suna na Hadoram
  5. Footnote Kaɗan a cikin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci, Seftuwajin da kuma Siriyak (dubi kuma 1Tar 18.12); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Aram (wato, Arameyawa).
  6. Footnote Ko kuwa su ne firistoci

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.