Skip to content
BibleKenya

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

1 Tarihi 1

Rubutaccen tarihi daga Adamu zuwa Ibrahim

Zuwa ’Ya’yan Nuhu Maza

(Farawa 5.1-32; 10.1-32; 11.10-32)

Adamu, Set, Enosh,

Kenan, Mahalalel, Yared,

Enok, Metusela, Lamek, Nuhu.

’Ya’yan Nuhu maza su ne,1 Shem, Ham da Yafet.

Mutanen Yafet

’Ya’yan2 Yafet maza su ne,

Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.

’Ya’yan Gomer maza su ne,

Ashkenaz, Rifat3 da Togarma.

’Ya’yan Yaban maza su ne,

Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.

Mutanen Ham

’Ya’yan Ham maza su ne,

Kush, Masar4 Fut da Kan’ana.

’Ya’yan Kush maza su ne,

Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.

’Ya’yan Ra’ama maza su ne,

Sheba da Dedan

Kush shi ne mahaifin5

Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.

Masar shi ne mahaifin

Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa, Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa.

Kan’ana shi ne mahaifin

Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa, Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa.

Semiyawa

’Ya’yan Shem maza su ne,

Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.

’Ya’yan Aram maza su ne,

Uz, Hul, Geter da Meshek.

Arfakshad shi ne mahaifin Shela,

Shela kuwa shi ne mahaifin Eber.

Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.

Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan.

Yoktan shi ne mahaifin

Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera Hadoram, Uzal, Dikla, Ebal, Abimayel, Sheba, Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.

Zuriyar Shem

(Farawa 11.10-26)

Shem, Arfakshad,6 Shela,

Eber, Feleg, Reyu

Serug, Nahor, Tera

da Abram (wato, Ibrahim).

Iyalin Ibrahim

(Farawa 25.1-4,12-16)

’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel.

Zuriyar Hagar

Waɗannan su ne zuriyarsu.

Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema Yetur, Nafish da Kedema.

Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza.

Zuriyar Ketura

’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne,

Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.

’Ya’yan Yokshan maza su ne,

Sheba da Dedan.

’Ya’yan Midiyan maza su ne,

Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a.

Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.

Zuriyar Saratu

Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku.

’Ya’yan Ishaku maza su ne,

Isuwa da Isra’ila.

’Ya’yan Isuwa maza

(Farawa 36.1-14)

’Ya’yan Isuwa maza, su ne,

Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora

’Ya’yan Elifaz maza su ne,

Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz,

da Timna wanda aka haifa wa Amalek.7

’Ya’yan maza Reyuwel su ne,

Nahat, Zera, Shamma da Mizza.

Mutanen Seyir a Edom

(Farawa 36.20-43)

’Ya’yan Seyir maza su ne,

Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.

’Ya’yan Lotan maza su ne,

Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan.

’Ya’yan Shobal maza su ne,

Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.

’Ya’yan Zibeyon maza su ne,

Aiya da Ana.

Ɗan Ana shi ne,

Dishon.

’Ya’yan Dishon maza su ne,

Hemdan, Eshban, Itran da Keran.

’Ya’yan Ezer maza su ne,

Bilhan, Za’aban da Ya’akan.

’Ya’yan Dishan maza su ne,

Uz da Aran.

Masu mulkin Edom

Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta.

Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.

Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.

Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.

Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.

Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.

Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.

Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.

Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab. Hadad shi ma ya mutu.

Manyan Edom su ne,

Timna, Alwa, Yetet Oholibama, Ela, Finon Kenaz, Teman, Mibzar, Magdiyel da Iram.

Waɗannan su ne manyan Edom.

Source notes (7)
  1. Footnote Seftuwajin; Ibraniyanci ba su da ’Ya’yan Nuhu maza.
  2. Footnote ’Ya’ya suna iya nufin zuriya Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 6-10, 17 da 20.
  3. Footnote Yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da na Bulget (dubi kuma Seftuwajin da Far 10.3); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Difat
  4. Footnote Wato, Masar; haka ma a aya ta 11.
  5. Footnote Mahaifi na iya nufin kaka ko wanda ya riga Ko kuwa wanda yake tushe; haka ma a ayoyi 11, 13, 18 da 20.
  6. Footnote Da Ibraniyanci; waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin suna da Arfakshad, Kainan (dubi kuma sharhi a Far 11.10).
  7. Footnote Waɗansu rubuce-rubucen hannun Seftuwajin (dubi Far 36.12); Ibraniyanci yana da Gatam, Kenaz, Timna da Amalek

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020. Copyright © Biblica, Inc. Licensed under CC BY-SA 4.0. Source: Open.Bible. Typeset from the source files; no intended changes to scripture wording. BibleKenya is not endorsed by the rights holder.

Full source notice & licence · CC BY-SA 4.0 · SourceEdition imported 2026-11-09.

BibleKenya

Reader settings

Theme
Font
Alignment
Reading width

Saved in this browser and used offline too. Press ? for keyboard shortcuts.